A wannan shekarar gwamnatin na shirin tura dailibai mata talatin kasar Sudan domin koyan aikin likita. Ayarin farko zasu kasance mata zalla ne kawai domin karancin likitoci mata da jihar ke fama da shi. Gwamnatin tace zasu dinga tura mata talatin kasar Sudan duk shekara kuma zasu kashe ko nawa ne kan harkokin ilimi domin ilimi shi ne gishikin kowace al'umma a duniya.
Da yake amsa tambayar da aka yi masa kwamishanan ilimi mai zurfi na jihar Bello Ayuba yace wannan somi ne. Kowace shekara za'a debi dalibai su je koyan aikin likita domin kada asibitocin jihar su rasa likitoci. Yace sun soma da mata ne domin suna da karancin likitoci mata a jihar fiye da yadda ake tsammani duk da cewa mata suka fi bukatar zuwa asibiti musamman batun haifuwa da kula da yara.
Da can gwamnatin ta tura wasu 25 Indiya koyan karatu. Yanzu suna cigaba a Ingila inda suke koyon tukin jirgin ruwa da aikin injiniya. Gwamnan ya tura mutane 20 su koyo aikin injiniyar man fetur.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.