Gwamnatin Najeriya ta sanar da kafa wani kwamiti wanda zai tabbatar da aiwatar da hukuncin da kotun koli ta yanke na bai wa kananan hukumomin Najeriya ‘yancin cin gashin kansu.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ne ya kaddadamar da kwamitin a ranar Talata wanda ya hada da ma’aikatun gwamnati.
Kudurin kwamatin shi ne a zartar da hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar 11 ga watan Yulin bana na ‘yantar da kananan hukumomin daga jihohinsu.
Daga cikin aikin kwamitin akwai ganin an tabbatar da cikakken ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi don su samu damar aiwatar da ayyukansu kamar yadda wata sanarwa da Darektan Yada Labaran ofishin Akume, Segun Imohiosen ya fitar ta ce.
“Wannan mataki ya yi daidai da kudurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ganin an aiwatar da hakan kamar yadda kundin tsarin mulki ya ayyana kananan hukumomi a matsayin matakin gwamnati na uku.” In ji Imohiosen.
A cewar sanarwar, Akume shi ne shugaban kwamitin, sauran wadanda za su yi aiki a kwamitin akwai gwamnan babban bankin Najeriya, Yemi Cardoso, wakilan gwamnoni, wakilan kananan hukumomi, Babban Akanta-Janar, Ministan Kudi da sauransu.
Dandalin Mu Tattauna