Ana zargin tsohon gwamnan ne da yin sama da fada da kimanin Naira miliyan dubu biyar mallakar jihar a lokacin da yake mulki.
Alkalin kotun Mai Shari'a Aliyu Maiyaki ya amince da bada belin tsohon gwamnan amma bisa sharudan bada Naira miliyan dari da hamsin da kuma mutane biyu masu tsaya masa wadanda suke da kaddarori ko kuma gidaje da kudadensu ya kai Naira miliyan dari biyu a Minna.
Kazalika tsohon kwamishanansa na ma'aikatar kula da muhalli Alhaji Umar Nasko da suke tsare tare ya samu beli akan Naira miliyan dari sannan da mutane biyu masu tsaya masa masu kaddarori ko kuma gidaje da kudadensu ya kai Naira miliyan dari da hamsin a Minna.
Daya daga cikin lauyoyin mutanen Barrister Mamman Usman yace sun ji dadin bada bellin amma sharudan belin sun yi tsauri da yawa kuma zasu basu wuyar cikawa. Sai dai Allah zai taimaka, inji shi.
Shugaban PDP a jihar Neja Barrister Tanko Beji yace makon da ya gabata ya fada cewa abun da Allah yayi zai yi maganinshi. Bayan mako daya Allah ya bada beli. Ya godewa Allah da magoya bayansu da suka tsaya shiru su saurari abun da kotu zata fada.
Tun can farko masu goyon bayan gwamnan suka yi dafifi a harabar kotun duk da yawan jami'an tsaron da aka jibge.
Alkalin zai cigaba da sauraren shari'ar ranar 12 ga watan gobe idan Allah Ya kai rai.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Facebook Forum