Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dillalan Takin Zamani Suna Bin Gwamnatin Tarayya Bashin Naira Biliyan 29


Wasu cikin Dillalan Takin Zamani dake bin gwamnati bashi.
Wasu cikin Dillalan Takin Zamani dake bin gwamnati bashi.

Wasu dillalan takin zamani da suke bin gwamnatin tarayya zunzurutun kudi har na Naira miliyan dubu ashirin da tara sun yi dafifi a gaban ma'aikatar gona suna kukan cewa rashin biyansu ya sa jarinsu ya kusa durkushewa

Dillalan da suka yi dafifi a gaban ma'aikatar gona sun samu kyakyawar karba daga sakataren ma'aikatar wanda yayi masu albishirin cewa za'a duba batun.

Dillalan na cewa bashin da suka ciwo daga bankuna na neman durkusar dasu sakamakon rashin biyansu a kan kari bashin Naira biliyan ishirin da tara da suke bin gwamnati..Akwai ma wani bashin na Naira biliyan goma tun bara na raba takin da wayar salula.

Kabiru Fara shugaban kungiyar dallalan yana mai cewa can baya ana gaya masu da baki za'a biya amma ba'a yi ba saboda haka su fito su bayyana masu da baki su kuma basu a rubuce shirin biyansu. Idan sun basu wa'adin biyan suka kuma wuce lokacin to duk abun da suka yi masu ruwansu, inji Kabiru Fara.

Dangane da abun da zasu yi idan ba'a biyasu ba, sai Kabiru Fara yace suna da zabi da dama. Akwai tafarkin siyasa kuma 'yan Najeriya sun gaji da yin alkawari babu cikawa. Zasu kuma rubuta a jaridu Shugaba Buhari ya gani domin ya san ba'a taimakon manoma.

Suna kuma da zabin su je kotu su ce sai an biyasu dole. Yace amma tunda suna da dangantaka da ma'aikatar gona basa son lamarin ya kaiga shari'a.

Alhaji Bello Abubakar Haliru Funtua mataimakin shugaban kungiyar manoman masara ta Najeriya yace taki yayi sauki a kasar saboda kafin wannan shirin da gwamnatin Buhari ta fito dashi sai da buhun taki daya ya kai Naira dubu goma.

Daya daga dillalan na karfafa a cigaba da shirin koda ba'a kammala biyansu ba. Yace don tashi ba za'a yi zanga zanga ba. Bai yi aikin domin Audu Ogbe ya biyashi ba. Yana cewa idan gwamnatin mai adalci ce zata biyashi ko bai bi sawu ba. Yace kamar yadda talakawa suka shaida Shugaba Buhari mai gaskiya ne duk ranar da ya farga suna bin gwamnati bashi za'a biyasu. Yace abun kunya ne a gwamnatin Buhari a ce talaka ya fito yana zanga zanga.

Yanzu dai gwamnatin Najeriya ta bada alkawarin biyan wasu kaso a cikin kudin nan da mako daya kamar yadda sakataren ma'aikatar gonan Bukar Hassan ya bada albishir.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG