A Africa ta kudu, wani kamfanin hakar ma'adinai ya ce ma'aikatansa bakwai sun mutu, an ceto wasu shida, bayan da girgizar kasa ta haddasa gocewar wani dutse a wani rami da ake hakar zinari.
Kamfanin da ake kira Sibanye Stillwater, ya fada jiya Asabar cewa ma'aikata 13 sun makale a ramin dake wuri da ake kira Masakhane a yankin Driefontain, bayan da girgizar mai karfin maki biyu da digo biyu ya afkawa yankin a ranar Alhamis.
Kamfanin yace ma'aikata shidan da aka ceto suna ci gaba da samun jinya a asibiti kuma basa cikin mawuyacin hali. Kamfanin ya ci gaba da cewa, shi, da ma'aikatar kula da ayyukan hakar ma'adinai, da wasu masu ruwa da tsaki zasu bincik lamarin.
Jami'an kasar ta fuskar kwadago sun bayyana damuwa kan matakan kare lafiyar ma'aikata a kamfanin da ake kira Sibanye.
Ahalinda ake ciki kuma,a Poand ma'aikatan hakar ma'adinai su biyu da suka bace, yanzu an gano su, amma sun jikkata. Lamarin ya auku ne bayan da girgizar kasa ta afkawa wani ramin tonon ma'adinai jiya Asabar akudancin kasar. Kuma har yanzu masu aikin ceto suna aiki domin kaiwa ga wasu ma'aikatan su biyar da suka bace a kamfanin na hakar ma'adinai.
Facebook Forum