Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Kano Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Sabbin Masarautu Masu Daraja Ta 2


Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)
Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)

Gwamana Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan kudirin dokar kafa masarautu ta bana da Majalisar Dokokin jihar ta zartar.

Dokar na da manufar mayar da masarautar Kano a matsayin mai daraja ta 1, a yayin da masarautun Rano da Gaya da Karaye zasu kasance masu daraja ta 2.

A cewar kudirin, sabuwar Masarautar Rano zata kunshi kananan hukumomin Rano da Bunkure da Kibiya, a yayin da Masarautar Gaya zata kunshi kananan hukumomin Gaya da Albasu da Ajingi, sai kuma Masarautar karaye da zata kunshi kananan hukumomin Karaye da Rogo.

Dukkanin masarautun masu daraja ta 3 guda 3 zasu kasance ne karkashin Sarkin Kano. Suna da ikon baiwa sarki shawara a al’amuran da suka shafi zaman lafiyar jama’a da rikicin kan iyaka da sasanta tsakanin al’umma da al’amuran addinin dake karkashin huruminsu.

Karara kudirin ya tsame Masarautar Bichi, wacce tsohon gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kirkira amma dokar masarautun kano da aka yiwa kwaskwarima a bana ta rushe ta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG