Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Kano Ya Bada Gudunmowar N100m Ga Mutanen Da Iftila’in Gobarar Kasuwa Ya Shafa


Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)
Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)

Ya mika gudunmowar ne yayin ziyarar da ya kai kasuwar, inda ya bayyana jajensa ga ‘yan kasuwar da al’amarin ya shafa.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika gudunmowar Naira miliyan 100 ga mutanen da iftila’in gobarar baya-bayan nan da ta afkawa kasuwar tufafi ta Kantin Kwari ya shafa.

Ya mika gudunmowar ne yayin ziyarar da ya kai kasuwar, inda ya bayyana jajensa ga ‘yan kasuwar da al’amarin ya shafa.

Gwamna Abba Yusuf ya kuma bayyana cewar manufar bada kudaden shine ragewa ‘yan kasuwar radadin iftila’in da ya samesu.

Ya kara da cewa, “duk da cewa kudaden ba zasu iya mayar da asarar da aka yi ba, amma manufar hakan ita ce taimakawa wadanda al’amarin ya shafa rage radadin iftila’in.”

Daukin gaggawar da jami’an kashe gobara suka kai ya taimaka wajen shawo kan gobarar da ta lalata shaguna 29.

Shugaban hukumar gudanarwar kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Sa’ad Hamisu Dogon Nama, ya bayyana godiya ga daukin da aka kawo musu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG