An yi kira ga duk wanda ya gudu ya bar gidansa a jihar Nasarawa da ya koma tare da tabbacin zamansa lafiya. Wannan kuwa ya biyo bayan wani gagarumin taron da aka yi tsakanin sarakunan gargajiya da shugabannin Fulani a jihar, inda aka baiwa juna hakuri da shawara, kuma kowane bangare ya yi alkawarin tabbatar da kwanciyar hankali da lumana.
Wakiliyarmu ta jihar Filato wadda ta aiko mana da wannan rahaton Zainab Babaji ta ruwaito Hakimin Fadamar Bauna ta Gabas daga Kabilar Eggon, Alhaji Ahmadu Adamu ya ce a yanzu hankula sun kwanta kuma ba wani bangaren da ke da wata matsala da kabilar Eggon. Ya ce sun bukaci a taimaka ma wadanda su ka rasa muhallansu saboda su koma su maido da rayuwarsu ta da kuma su iya yin zabe to amma har yanzu su na saurare. Ya ce wani abin da ke hana wasu komawa gidajensu a jihar kuma shi ne abin da ke faruwa a sassan kasar amma ba a jihar ba.
Haka zalika, Sarkin Kwandare Alhaji Ahmadu Almakura ya ce sun shafe shekara guda suna ta taro har sau 27, amma a yau an shirya tsakanin dukkannin bangarorin bisa jagorancin gwamnatin jihar. Y ace yance kowa na komawa muhallinsa cikin kwanciyar hankali ba tare da wata fargaba ba.