Take shahararren Malamin addinin Musulunci Sheikh Tijjani Bala Kalarawi yayi kira ga jama’a.
“Masu hannu da shuni su taimakawa bayin Allah wadanda basu da shi. Wadanda suke da manyan shaguna na sayar da kaya, shekara guda sun samu riba, su godewa Allah. Wannan wata mai albarka, su saukaka wa bayin Allah da basu da shi, don suma Allah Yayi murna da irin alkhairin da Ya basu, sun nuna sun gode masa.”
Sheikh Abdullahi Bala Lau yace a dage da yiwa kasa addu’a a cikin wannan wata da kan share kwanaki 29 ko 30.
“Ba wata bane na zama a yi lido da karta, Annabi ya hana a sauke Qur’ani kasa da kwana uku, amma yace halal ne a cikin Ramadan.”
‘Yan siyasa ma irin su dattijon PDP barayan Bauchi Sunusi Baban Tanko na gani ya kamata jingina banbancin jam’iyya domin yiwa kasa fatan Alheri.
Sakataren kungiyar Jama’atu Nasirul Islam Dr. Khalid Aliyu yayi wa malamai nasiha.
“A ji tsoron Allah, a yi tafsiri saboda Allah. Ba a mayar da wajen tafsiri kamar wani dandali na cin mutuncin wasu ko na kushe wasu, ko na bata wasu ba.”
Tuni malamai suka fara gabatar da tafsirin al-Qur’ani mai girma.