Kasa da kwanaki biyu da babban Hafsan sojan Najeriya ya Laftanar Janar Tukur Buratai, yace in tattaunawa da tsagerun Niger Delta bai samu nasara ba to babu makawa za a yi amfani da karfin soja.
Cikin martanin da ya mayar gwamnan jihar Bayelsa Mr. Serieki Dickson, ya yin da yake tattaunawa da ‘yan jaridu a birnin tarayya Abuja yace sam sam baya goyon bayan amfani da karfin soja.
Yace “in an duba wannan yanayi da tarihin wannan kalubale to amfani da karfin soja bashi zai magance matsalar ba. mu shugabannin siyasar wannan yanki aikin mu ne mu shawo kan al’ummar mu, amma a gano musabbabin wannan matsala ma tukunna, kamar yadda nake fada amfani da karfin soja ba itace hanyar da ta dace ba.”
Sai dai kuma Dakta Abubakar Umar Kari, wanda yake malami a jami’ar Abuja na ganin cewa martanin na gwamna Dickson, ya yi shine saboda idan akayi amfani da karfin soja al’ummarsa ne zasu shiga wani hali. Haka kuma Dakta Kari, na ganin maganar da Buratai ya fada itace ra’ayin mafiya ‘yan Najeriya.
Saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.