Shugaban hadakar 'yan majalisun tarayyan Sanata Suleiman Nazif Gamawa ya bayyanawa taron 'yan jarida cewa sun kafa wani kwamiti da zai sa ido akan lamuran gwamnatin jihar tasu.
Yace ya zama alatilas garesu su hada kansu domin su ceto Bauchi saboda haka suka kafa kwamitin da zai sa ido a alamuran jihar da zummar hana almundahana da coge da ake yi.
Sanatan ya kira duk wani dan jihar da ya san ana almundahana ko kuma ana coge ko kuma akwai wani abun da ya ga ba daidai ba ya rubuta korafinsa zuwa EFCC dake Abuja kana ya ba kwamitin abun da ya rubutawa EFCC. Su 'yan majalisan wakilan zasu dauki mataki akan korafin.
Akan cewa sun ki karbar gayyatar gwamnan wanda yace su zauna domin su lalubo bakin zaren matsalar, Sanata Nazif yace ba zasu amince da yadda gwamna ya kawo jam'iyyar ofishinsa ba ta yadda an kasa gane jam'iyya daga gwamnati. Gwamnan ya hada gwamnati da jam'iyya ya rike a gidan gwamnati.
Akam maida martani mai ba gwamnan shawara kan harkar jarida Sabo Muhammad yace suna jiran lokaci. Suna jiran su ji abun da zasu ce. Gaskiya zata yi halinta.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.