Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Masu Coronavirus Ya Karu a Amurka


Mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence yayin da ya ke magana a wani taro kan Coronavirus.
Mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence yayin da ya ke magana a wani taro kan Coronavirus.

Rahotanni na nuni da cewa an samu karin mutum hudu da cutar Coronavirus ta kashe a Amurka, duk kuwa da cewa a yankin da cutar ta fi kamari wato China adadin ya yi kasa sosai cikin makonni shida da suka gabata.

An kuma sallami daruruwan mutanen da suka kamu da cutar daga Asibitoci.

Mutuwar da aka samu a jihar Washington da ke yammacin Amurka ta sa yawan wadanda suka mutu dalilin cutar ya kai shida.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da cutar ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya, ciki har da kusan mutum 100 da suka kamu da cutar a nan Amurka.

A wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fitar, an samu karin wadanda suka kamu da cutar a wajen China da kusan ninki tara fiye da wadanda ake samu a China, bayan da aka samu rahotan cutar a birnin New York, Berlin da kuma Moscow.

Yawan wadanda cutar ta kashe ya wuce 3000 a yanzu, kuma yawan mutanen da suka kamu a kasashe 60 ya haura zuwa sama da 89,000.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG