WASHINGTON DC, —
A bangaren muna salon karin Magana, Dr. Abubakar Garba Imam, yayi muna karin haske ne a kan karin Magana mai korewa tare da sharadi. Yabada misali kamar yadda ake cewar, idan kaji ance mutun bai iya kukaba to uwashi bata mutu bane, anan za’aga cewar ai don bai iya kukaba amma sai akace dalili kuwa shine don uwashi bata mutu bane shiyasa bai iya kukan ba. Don kuwa duk randa akace ta mutu to lallai zai iya kukan.
Kana kuma ya kara da wani misali, idan kaji mutun yace bai iya guduba, to ba’a rikeshi bane shiyasa. Amma da zarar an rike mutun to bai zai san sanda zai kubuce ba har yafara gudu. Akwai karin Magana masu korewa a wasu lokkuta da dama da mutane kanyi amfani dasu, masu ma’ana.