WASHINGTON, DC —
Wadanda suka yi garkuwa da 'yan biyun nan a jihar Zamfara dake shirin aure, sun sake su bayan wata daya da sace su, Hakan ta faru ne bayan biyan Naira miliyan goma sha biyar kudin fansa. Saurari shirin domin karin bayani.
Shirin Domin Iyali har wa yau, yayi hira da 'yar takarar shugaban kasa karkashin tututar jam'iyar Allied Congress Party of Nigeria, ACPN, Tsohuwar Mataimakiyar babban bankin Duniya wadda kuma take daya daga cikin wadanda suka fara fafatukar ceto 'yammatan Chibok har wa yau tsohuwar ministar ilimi a Najeriya Dr Oby Ezekwesili. A cikin doguwar hirarta da wakiliyarmu Madina Dauda, Madam Oby ta fara da bayyana abinda ya banbanta ta da sauran 'yan takara.
Saurari cikakken shirin
Facebook Forum