Bayan tabbatar da cewa kungiyar mayakan ta kashe Hauwa Liman ‘yar shekaru ishirin da hudu wadda take aiki da kungiyar agaji ta kasa da kasa da ake kira “International Committee of Red Cross", shugaba Muhammadu Buhari ya kira iyayen yarinyar ta wayar tarho yayi masu jaje, Ya kuma bayyana takaicin ganin yunkurin gwamnatin na ceto ta da sauran wadanda kungiyar ta sace bai kai ga ceto ta ba.
Banda kungiyar agaji ta Red Cross da ta yiwa aiki, kungiyoyi a ciki da wajen Najeriya sun yi ta hurawa gwamnatin tarayya wuta musamman bayan barazanar da kungiyar Boko Haram tayi na kashe ma’aikaciyar idan ba a cika sharuddan da ta gindaya ba cikin lokacin da ta ayyana. A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar bayan kashe ma’aikaciyar, da aka yayata a jaridun ciki da wajen Najeriya, tace zata bar Leah Sharibu da rai ta rika yi mata aikin bauta.
Da yake tabbatar da labarin, ministan watsa labarai na Najeriya, Lai Mohammed ya bayyana kisan a matsayin rashin Imani, ya kuma ce gwamnati zata ci gaba da yin iyaka kokari domin ganin an sako sauran mutanen da kungiyar take garkuwa da su.
Ranar jumma’a da ta gabata, karon farko, tawagar gwamnatin tarayya, karkashin jagorancin ministan watsa labarai, Lai Mohammed ta ziyarci mahaifiyar Leah, Rebecca Sharibu a garin Dapchi hedkwatar KRH Bassari.
Ministan ya jadada aniyar gwamnatin tarayyar Najeriya na ceto Leah ko duk da cikar wa’adin da kungiyar ta bayar na neman gwamnati ta cika sharudddan da suka gindaya ko kuwa su hallaka ta.
Lai Mohammed ya jadada cewa gwamnati tana iya kokari domin ganin an ceto Leah.
A nata jawabinta mai sosa rai, cikin hawaye, mahaifiyar Leah ta sake jadda kira ga gwamnatin tarayya ta ceto Leah.
Saurari cikakken shirin:
Facebook Forum