Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gombe: Zaben dan majalisar wakilan Najeriya a Akko ya bar baya da kura


Shugaban INEC Mahmud Yakubu
Shugaban INEC Mahmud Yakubu

Zaben da kotu ta bada umurnin a sake gudanar dashi da aka yi a Akko ya bar baya da kura saboda APC ta ki amincewa da sakamakon wanda ya ba PDP nasara

Jam'iyyar APC dake adawa a jihar Gombe ta garzaya kotu tana kalubalantar sakamakon da hukumar zabe ta INEC ta bayar wanda ya ba dan PDP nasara.

Ita APC tana kalubalantar sahihancin zaben da kuma hanata yin takara.

Kakakin hukumar zabe ta INEC ta bakin kakakinta Muktar Gidado tace Ismail Hassan Kashere na PDP ne ya ci zaben. Dama takarar tsakanin PDP ne da SDP.

Da yake mayarda martani akan sakamakon zaben dan takarar jam'iyyar APC Alhaji Umaru Barambu ya yi watsi da sakamakon. A cewarsa zaben tamkar ba'a yi shi ba saboda haka sun garzaya kotu. Babu yadda za'a yi a fitar da jam'iyya guda daga zabe.

Amma inji Alhaji Ali Isa Jesi dan majalisar wakilai na tarayya daga mazabar balanga kuma dan jam'iyyar PDP yace zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali kuma basa fargaban shiga kotu

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG