‘Yan majalisar Dattawan Amurka suna shirye-shirye kada kuri’a a gobe Alhamis, akan wasu bukatu biyu da ‘yan Republican da ‘yan Democrat suka gabatar daban-daban a gaban majalisar, wadanda ke neman a kawo karshen dakatar da ayyukan wasu ma’aikatun gwamnatin kasar.
Tuni dai ‘yan jam’iyyar Democrat masu rinjaye a majalisar wakilai suka amince da dokar da za ta samar da kudaden da za a tafiyar da wasu ma’aikatun gwamnati har zuwa 8 ga watan Fabarairu.
Ana sa ran wannan mataki zai ba da damar a bude ma’aikatun gwamnatin yayin da bangarorin biyu za su ci gaba da muhawara kan samar da tsaro akan iyakar Amurka.
Sai dai a cikin kasafin kudin na ‘yan jam’iyyar Democrat babu kudin da shugaba Donald Trump yake bukata na gina katanga tsakanin kan iyakar Amurka da Mexico.
Amma kasafin kudin ‘yan Republican yana kunshe da bukatar da shugaba Trump yake so ta kashe dala biliyan 5. 7 akan katanga da kuma bai wa wasu baki da suka shigo Amurka ba bisa ka’ida ba kariya ta wani dan takaitaccen lokaci.
Fadar White House ta ce, shugaba Trump ya shirya tattaunawa akan shirinsa na gina katanga tsakanin Amurka da Mexico a yau Laraba, tare da shugabanni masu ra’ayin mazan jiya har da na jiha da kuma sauran shugabanin kananan hukumomi.
Facebook Forum