Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rufe Kasuwar Wuse Sakamakon Bindige Wani Dan Kasuwa Ya Janyo Kace Nace


An Samu Hargitsi Yayin Da 'Yan Sanda Su Ka Harbe Wani Dan Kasuwa A Wuse Abuja
An Samu Hargitsi Yayin Da 'Yan Sanda Su Ka Harbe Wani Dan Kasuwa A Wuse Abuja

An samu barkewar hayaniya a yau Laraba biyo bayan rufe shahararriyar kasuwar Wuse a Abuja da hukumar gudanarwarta tayi sakamakon tashin gobara a cikinta a jiya Talata.

ABUJA, NAJERIYA - Rahotanni na cewar al'amarin yayi kamari, bayan da aka ga wasu mutane da suka ki barin kasuwar rike da fasassun kwalabe da sanduna.

Sa'ilin hada wannan rahoton, jami'an 'yan sanda da takwarorinsu na rundunar tsaron sibil difens sun isa kasuwar domin dawo da doka da oda.

In ba'a manta ba, jiya ne hargitsi ya barke a kasuwar bayan da 'yan sanda su ka bude wuta da ya kai ga mutuwar wani dan kasuwa.

Al'amarin ya auku ne bayan kama dan kasuwar da kuma yanke ma sa hukuncin tafiya gidan yari saboda kasa kaya barkatai.

Wani ganau ya bayyana yanda akasin ya auku, inda jami'an 'yan sanda na kwamitin aiki da cikawa su ka kama dan kasuwar da mika shi ga kotun tafi da gidan ka wacce ta yanke ma sa hukuncin tafiya gidan yari.

Lokacin da 'yan sanda su ka saka mutumin mai suna Oga Musa a mota sai ya yi tsalle ya diro daga motar don arcewa inda 'yan sanda su ka harbe shi ya mutu nan take.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG