Da farko jami’ai sunce mutane tamanin da biyar ne suka mutu, a hadarin da ya auku ranar laraba, sai dai yau jumma’a adadin ya haura ainun. Gobarar ta auku ne a kan wata hanya dake kusa da garin Maridi, mai tazarar kilomita dari biyu da hamsin da Juba babban birnin kasar.
Mariam Tito, shugabar lardin Mambe Mayan ta shaidawa wani shirin Muryar Amurka “South Sudan In Focus” cewa, mai yiwuwa ne adadin wadanda suka rasu ya karu kasancewa mutane da dama sun yi mummunar kuna.
Irin wannan fashewar tana yawan aukuwa a kasar ta gabashin Afrika da talauci ya yiwa katutu, inda mutane suke dafifi idan motar dakon mai tayi hadari,suna satar mai. A watan Yuni shekara ta dubu biyu da goma sha uku,, mutane talatin suka mutu a wata gobarar motar dakon mai a kasar Uganda.