Mutumin da aka nada domin ya jagoranci hukumar da masu juyin ke kira “Majalisar Jaddada Akidar Demokaradiya”, Brig-Janar Gilbert Diendere, tsohon na hannun daman tsohon shugaban Burkina Faso din ne, Blaise Campaore wanda shima boren jama’a na bara ya janyo sanadin hambare shi daga karagar mulkin da ya share shekaru 27 akanta.
A yau ne wani jami’in soja ya fito a cikin telebijin yana bada sanarwar cewa an tumbuke gwamnatin ta Burkina, kuma an cirewa shugaban gwamnatin wucingadi na kasar Michel Kafando rigarsa ta mulki. Kuma har yanzu Kafando din da Firai ministan kasar suna tsare a hannun sojan da suka cafke su lokacinda ake wani taron majalisar ministoci jiya Laraba a can birnin na Ouagadougou.
Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta la’anci wannan juyin mulkin inda kuma ta nemi a sako mutanen da aka tsare. Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon yace al’amarin, wanda ya bayyana da cewa “taka kundin tsataka kundin tasrin mulkin kasar ne
Bayanda sojojin dake kula da tsaron fadar shugaban kasar Burkina Faso suka bayyana cewa,sun gudanar da juyin mulki a kasar, wakilinmu na birnin Yamai a Janhuriyar Nijar mai makwabtaka da kasar da Burkina Faso Yusuf Abdullahi ya samu zantawa da shugaban Muryar talaka a Nijar Nassiru Saidu wanda a cikin wannan hirar ya soma da yin kira da kasahen duniya na ganin sun tilassawa sojojin barin mulki.
Ga cikakken bayanin Mal Nassiru