Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirka ta Tsakiya: Paparoma Ya Kira Bangarorin dake Fafatawa Su Rungumi Zaman Lafiya


Paparoma Francis Bangui babban birnin Afirka ta Tsakiya
Paparoma Francis Bangui babban birnin Afirka ta Tsakiya

Paparoma Francis ya yi kira ga bangarorin da ke yaki da juna a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da su ajiye makamansu, su kuma rungumi hanyar da aka dauka domin kawo karshen rikicin.

A jiya Lahadi Paparoman ya isa Bangui, babban birnin kasar, domin gabatar da sakon zaman lafiya ga kasar da rikicin siyasa ya rikide ya koma na addini tsakanin kiritsa da musulmi.

Yayin da ya ke gabatar da jawabinsa a wani taron addu’a a mujami’ar Cathedral da ke Bangui, Paparona Francis, ya yi kira ga wadanda suke rike da makamai, da su ajiye “makaman mutuwa” kamar yadda ya kwatanta.

Ya ce a maimakon rike makamai, ku shirya kanku da dabi’u masu kyau da kauna da tausayi, wadanda sune ginshikan zaman lafiya.

Gabanin wannan jawabi nasa, Paparoman ya kuma yi kira ga dukkanin bangarorin, da kada su bari banbancin addini ya raba kawunansu, ya kuma yi fatan zaben da ke tafe zai baiwa kasar dama ta bude sabon babi a tarihinta.

Kafin zuwan Paparoman, Shugaba Catherine Samba Panza ta bayyana a ranar Asabar cewa, mutane na yiwa shugaban na mabiya darikar Katolika kallon mai sakon zaman lafiya.

Kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika ta kwashe kusan shekaru uku tana fama da tashe-tashen hankula, tun bayan da ‘yan tawayen Seleka wadanda mafi aksarinsu musulmai ne suka hambarar da gwamnatin Francois Bozize a watan Maris din shekarar 2013 suka rinka cin karensu ba babbaka.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG