Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara A Babbar Kasuwar Gusau Ta Kashe Mutum Daya


Babbar kasuwar Gusau da wasu shaguna suka kama da wuta
Babbar kasuwar Gusau da wasu shaguna suka kama da wuta

Wata gobara da ta tashi ta lalata shaguna da dama a babbar kasuwar Gusau, na jihar Zamfara a Najeriya, inda ta kashe mutum daya.

WASHINGTON, D. C. - Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe tara na daren jiya a bangaren kayan daki na babbar kasuwar a babban birnin jihar.

Kwamandan hukumar kashe gobara ta Najeriya a ofishin sabuwar kasuwa, Hamza Mohammed ne ya sanar da gidan talabijin na Channels cewa wani mai shago wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba ya mutu a lokacin da yake kokarin shiga shagonsa da domin kashe gobara.

Jami’an kashe gobara na rundunar ‘yan sandan jihar sun yi ta fafatawa da gobarar tun karfe tara na daren jiya, don hana yaduwa zuwa wasu shaguna a kasuwar.

Mohammed ya fadi cewa gobarar ta shafi shaguna da dama, amma har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba da yawan dukiyoyi da aka yi asararsu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG