Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Glasgow: Buhari Na Halartar Taron Kasashen Duniya Kan Sauyin Yanayi


Lokacin da Buhari ya isa birnin Glasgow (Hoton bidiyo/Fadar shugaban kasa)
Lokacin da Buhari ya isa birnin Glasgow (Hoton bidiyo/Fadar shugaban kasa)

A ranar Talata 2 ga watan Nuwamba Buhari zai gabatar da jawabinsa a gaban taron kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar ta ce.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa birnin Glasgow da ke Scotland don halartar taron koli da shugabannin kasashe sama da 100 ke halarta don tattauna matsalar sauyin yanayi.

Buhari ya bar Najeriya a ranar Lahadi don halartar taron wanda Firai Ministan Burtaniya Boris Johnson ke jagoranta tare da hadin gwiwar kasar Italiya.

A ranar Talata 2 ga watan Nuwamba Buhari zai gabatar da jawabinsa a gaban taron kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar ta ce.

Cikin jawabin da zai gabatar, ana sa ran zai tabo muhimman matakan da Najeriya ke dauka wajen yaki da sauyin yanayi da kuma yunkurin da kasar ke yi na dora tattalin arzikin Najeriya kan turbar amfani da matakan dakile gurbata muhalli, wadanda za su yi daidai da matsayar da aka cimma kan manufofin yaki da sauyin yanayi a Paris.

“Lura da irin jagorancin da Najeriya ke yi da wannan matsala kuma a matsayinta na kasa wacce ke cikin yarjejeniyar Paris, wannan taro zai ba wakilan Najeriya wata dama su yi aiki da takwarorinsu na sauran kasashe don cimma muradun wannan taro, wadanda suka hada da takaita gurbata yanayi zuwa maki 1.5” In ji Garba Shehu.

Wannan taro da ke yi a karo na 26, ya tattaro masu ruwa da tsaki da suka rattaba hannun kan yarjejeniyar da ake kira COP26 karkashin wani jadawali da Majalisar Dinkin Duniya ta shimfida kan yadda za a tunkari matsalar sauyin yanayi a duniya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG