Wata girgizar kasa mai karfin gaske, ta fadawa yankin arewa maso gabashin Venezuela, inda ta girgiza gidaje, ta kuma sa mazauna yankin suka fita daga muhallansu zuwa kan tituna domin tsira da ransu.
Hukumar da ke nazarin yanayin karkashin kasa ta Amurka, ta ce girgizar kasar mai karfin maki 7.3, ta abkawa yankin da zurfin kilomita 123.
Yankin da bala’in ya fi shafa, na da nisan tafiyar kilomita 20 daga arewa maso yammacin garin Yaguaraparo.
Shugaban sashen kashe gobara a Caracas, John Boquett, ya ce, rahotannin da suka samu na farko sun nuna cewa babu wanda ya ji rauni ko kuma wata gagarumar barna da ta auku a birnin na Caracas.
Wannan bala’i na girgizar kasar, an ji hucinsa har a Bogota, babban birnin Colombia, lamarin da har kai ga hukumomin yankin suka sa aka rufe filin tashin jirage na dan wani lokaci, domin a kaucewa bacin hanyar da jirgi ke tashi.
Babu dai bayanai da ke nuna cewa an samu asarar rayuka ko barna a wannan girgizar kasa, sannan babu sakon gargadi da aka aike na yiwuwar aukuwar bala’in Tsunami.
Facebook Forum