Amurka ta saka takunkumin tattalin arziki akan Venezuela a jiya Litinin, saboda abinda ta kira “magudin zabe da aka tafka” a wajen sake zaben shugaba Nicolas Maduro a wa’adin na biyu na tsawon wasu shekaru shida.
Shugaba Trump ya sanya hannu akan wata doka ta shugaban kasa-da zai iya dauka wani umurni na kashin kansa ba tareda izinin majalisa ba, wanda ya haramtawa Amurkawa yin cinikayyar man fetur da kasar ta Venezuela, wacce a da, tana daya daga cikin kasashen duniya da ke gaba-gaba wajen samar da man na fetur.
Hukumomin a Caracas, babban birnin kasar ta Venezuela sun soki labarin takunkumin, inda ministan harkokin kasashen waje, Jorge Arreaza, ya fadawa manema labarai cewa, matakin na Amurka haramatacce ne, yana mai kwatanta shi a matsayin “hauka, gidadanci da kuma keta dokokin kasa da kasa.”
Facebook Forum