A yau Litinin kafar yada labarai ta Iran ta bada rahoton cewa mutane 328 ne suka mutu, kuma yawancin waddanda bala'in ya rutasa da su mazauna garin da ake kira Sarpol-e-Zahab a lardin Kermanshah.
Masu aikin ceto da agaji sun yi ta aiki a cikin daren har zuwa yau Litinin domin taimakwa waddanda girgizan kasar ta afkawa.
Hukumar kula da yanayin karkashin kasa ta Amurka ta ce karfin girigizar ya kai maki 7.3, kuma ta samo asali ne a kusa da garin Halabja a yankin Kurdawan Iraqi.
Frime Minista kasar Haidar al-Abadi, ya ce ya umarci hukumomin kiwon lafiya da na agaji, su dauki dukkan mataki na taimakawa wadanda bala'in ya shafa
Facebook Forum