Shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akuffo Addo, a jawabin da ya fitar ga manema labarai ya ce "A madadin al'ummar Ghana, ina mika sakon ta'aziyyata ga Sarki Mohammed VI da gwamnati da kuma al'ummar Masarautar Maroko kan ibtila’in girgizar kasa da ta afku a ranar Juma'a ta kuma yi sanadin mutuwar dubban mutane."
Shugaban Akufo-Addo ya kara da cewa, Ghana na yi wa iyalan wadanda abin ya shafa addu’a, kuma Maroko za ta iya dogaro da goyon bayan Ghana a wannan mawuyacin lokaci da take ciki.
Mataimakin shugaban kasa, Dakta Mahamudu Bawumia, ya rubuta jajensa a shafinsa na Facebook cewa "Ta'aziyyata ga Sarki Mohammed VI da al'ummar Maroko, bisa mummunar girgizar kasa da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama, tare da jikkata wasu da dama. Tunanina da addu'o'ina suna tare da mutanen Maroko a cikin wannan mawuyacin lokaci na bakin ciki."
Shi ma Limamin limamai na Ghana, Dakta Shaikh Usman Nuhu Sharubutu, a jawabin da ya fitar ga manema Labarai, ya rubuta cewa "Girgizar kasa, ibtila’i ne da ke bukatar hadin kan duniya wajen taimaka wa Maroko."
Ya yi kira ga gwamnatin Ghana, shugabannin duniya da kungiyoyin kasa da kasa da su nuna wa Masarautar da kuma iyalan da abin ya shafa kauna da kulawa yayin da suke fafutukar jure wa lokutan wahala, kamar yadda Dakta Mohammed Marzuq, mataimaki na musamman ga Shaikh Usman Sharubutu ya yi karin bayani ga Muryar Amurka.
Shugaban gidauniyar sarkin Maroko kungiyar Mohammed Sadis na Malaman Afirka reshen Ghana, Shaikh Mustapha Ibrahim ya yi kira da a yi wa kasar addu’a.
Pastor Felix Nze, limamin cocin Author of Fire Prayers and Deliverance Ministry dake Accra da Malam Khamis Khalil sun jajanta wa al’ummar Maroko.
Girgizar kasar mai karfin 6.8 a ma'auni da ta afku a tsaunukan Atlas ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da 2,900 ya zuwa ranar Talata, tare da wasu 2,500 da suka jikkata, in ji ma'aikatar cikin gidan Maroko. Har wa yau ana ci gaba da neman wadanda suka tsira da kuma gawarwaki.
Saurari rahoton Idris Abdullah:
Dandalin Mu Tattauna