Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Gas Na LNG Ya Ce Samar Da Iskar Gas Ya Gamu Da Cikas Saboda Satar Mai


Jirgin LNG
Jirgin LNG

Kamfanin Nigeria LNG Ltd yana samar da kashi 68% ne kadai saboda satar danyen mai da lalata bututun mai da dai sauran matsaloli, inji shugaban kamfanin a ranar Talata.

Kamfanin na LNG, hadin gwiwa ce tsakanin kamfanin man fetur na kasa na Najeriya, da kamfanin Eni (ENI.MI), da TotalEnergies (TTEF.PA) da na Shell (SHEL.L) mai karfin tan miliyan 22 a kowace shekara.

Babban jami’in gudanarwa Philip Mshelbila ya ce sannu a hankali sata da barna suna dabaibaye harkar man fetur da iskar gas a Najeriya.

"Mun yi ta samar da mai tsakanin kashi 60 zuwa 68 cikin dari a cikin watan da ya gabata," kamar yadda ya shaida wa taron makamashi a Abuja.

“Akwai dalilai da dama, amma babban daya daga cikinsu shi ne satar danyen mai, idan ba mu magance wannan ba, ba za mu fita daga cikin wannan kuncin da muke ciki ba."

Mshelbila ya ce kamfaninsa ya dakatar da fitar da iskar gas da ake sayarwa kasashen waje domin amfanin cikin gida don biyan bukatar da ake samu daga kasuwannin cikin gida.

Hukumar kula da albarkatun man fetur ta Najeriya ta ce a makon da ya gabata kasar ta yi asarar dala biliyan 1 na kudaden shiga a cikin kwatar farko na wannan shekara sakamakon satar danyen mai, inda ta yi gargadin yin hakan barazana ce ga tattalin arzikin kasar da ke kan gaba wajen samar da mai a nahiyar Afirka.

~ REUTERS

XS
SM
MD
LG