Baldwin na magana ne a Najeriya inda ya gana da jami'an hukumar da ke hako man fetur a Najeriya a cikin makon nan.
An shaida masa cewa Najeriya na inganta tsaro a yankin Neja Delta, kuma tana shirin sake bude bututun mai na Trans Niger bayan watan Agusta, wanda zai samar da karin iskar gas zuwa kasashen Turai.
Baldwin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho cewa Tarayyar Turai na shigo da kashi 14% na jimillar kayan da take amfani da shi na LNG daga Najeriya kuma akwai yuwuwar ninka wannan.
Ana fama da matsalar man fetur da iskar gas a Najeriya ta hanyar sata da lalata bututun mai, lamarin da ya sanya tashar samar da iskar gas ta Nigeria LNG Ltd dake tsibirin Bonny ke aiki da kashi 60%.
"Idan za mu iya kaiwa sama da kashi 80%, a wannan lokacin, za a iya samun ƙarin iskar gaz da za a iya samu don jigilar kayayyaki zuwa Turai," in ji Baldwin.
"Su ( jami'an Najeriya) sun ce mana, 'Ku zo mu sake tattaunawa a karshen watan Agusta domin muna tunanin za mu iya kawo ci gaba na gaske a kan wannan fanin."
Hukumar Tarayyar Turai ta fada a ranar Laraba cewa, ya kamata kasashe mambobin kungiyar su rage yawan iskar gas da suke amfani da shi da kashi 15 cikin dari daga watan Agusta zuwa Maris.