Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GHANA - Hukumar Tabbatar Da Wanzuwar Zaman Lafiya Ta Bukaci A Rufe Wasu Gidajen Rediyo Saboda Hura Wutar Rikici A Bawku


Majalisan tabbatar da wanzowar zaman lafiya a Ghana ta National Peace Council
Majalisan tabbatar da wanzowar zaman lafiya a Ghana ta National Peace Council

Hukumar tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a Ghana da ake kira National Peace Council ta bukaci gwamnati ta dauki matakin ladabtar da wasu gidajen rediyo a yankin Bawku da ke gabashin Ghana.

Hukumar ta yi hakan ne bisa zargin cewa gidajen rediyon da suka hada da Bawku FM, da Source FM na hura wutar rikici tsakanin kabilu biyu na yankin da basa ga maciji.

Kiran bukatar a rufe gidajen rediyon na zuwa ne biyo bayan wani rikicin kabilanci a yankin da ya kai ga hasarar dukiyar gwamnati tare da kashe wasu da basu da alaka da kabilun da ke fada.

"Gidajen rediyo ne guda biyu. ko wane zance ya taso ko da karamin abu ne, idan dai ba zai zama alheri ga wani bangare ba, to bai kamata gidajen rediyon su ruruta wutar rikici ba. A dalilin haka ne ya sa hukumar ta bukaci a rufe gidajen rediyon a wani mataki na shawo kan wannan rikici," a cewar Sheikh Salman Alhassan, Mamba a hukumar ta wanzar da zaman lafiya a kasar.

Muhammad Nurudeen Abubakar Ali, mai fafutukar kare hakkokin bil'adama a Ghana, na ganin muddin rufe gidajen rediyon shi ne abinda zai kawo zaman lafiya to ya kamata hukumomi su yi aiki da wannan shawara.

Shugaban sashen kula da shirye shirye a gidan rediyon Bawku FM Muhammad Abdul Samad, wato daya daga cikin gidajen rediyo da ake zargi, ya musanta zarge-zargen.

"Gidajen rediyon basu da hannu a rikicin kabilancin Bawku kuma babu wani gidan rediyo da ke da alaka da wata kabila da ke fada. A don haka wannan zargi babu kanshin gaskiya a cikinsa," a cewar Abdul Samad. Ya kara da cewa, a gidan rediyon Bawku FM, an kirkiro wani shiri da ke da'awar zaman lafiya a Bawku a matsayin gudunmuwa wajen kawo zaman lafiya.

Wasu munanan hare hare da aka kai a baya bayan nan sun yi sanadiyar kisan wasu 'yan kabilun da basu da alaka da rikicin kuma 'yan bindiga sun lalata dukiyar gwamnati, ciki har da na'urar lantarki da ta kashe gobara a yankin.

Shu'aibu Musah Gutare, shugaban kungiyar kabilar Busangawa a Ghana, ya fada wa manema labarai cewa ana kashe 'yayan kabilarsu da basu san hawa ba basu san sauka ba a Bawku ya kuma bukaci gwamnati ta dauki mataki.

"Lamarin yayi tsanani sosai, saboda ba a wuce sati ba tare da an kai wa 'yan kabilarmu hari ba. A baya bayan nan sai da aka harbe wasu mutun 5 'yan zuri'a daya har lahira, ciki har da dan shekara 12 da haihuwa," a cewar Gutere.

Wakilin Muryar Amurka Hamza Adam a Ghana, ya yi kokarin ji ta bakin shugaban hukumar tsaro a gundumar Bawku game da wannan lamari amma abun ya ci tura.

XS
SM
MD
LG