Kungiyar kwallon Kafa ta Swansea City dake kasar Ingila ta bayyana sunan Graham Potter a matsayin sabon Kocin kulob din inda zai jagoranci kungiyar bisa yarjejeniyar kwantirakin shekaru uku masu zuwa.
Potter, mai shekaru 43 a duniya ya je kungiyar ta Swansea City ne daga tsohon kulob din sa dake kasar Sweden, inda dukkan kungiyoyin biyu suka cimma daidatuwa kan batun.
Kocin Graham Potter, ya maye gurbin tsohon Kocin Swansea ne Carlos Carvalhal wanda kungiyar ta sallameshi sakamakon rashin kare darajarta a gasarar Firimiya lig ta bana a kasar Ingila, inda yanzu zata buga gasar kasa da Firimiyan mai suna championship.
Swansea ta ce ta dauko Potter, ne domin ya farfado da martabar kungiyar a idon duniya da kuma magoya bayanta wajan ganin ta dawo cikin gasar Firimiya lig a shekara mai zuwa.
Sabon Kocin ya ce zasu yi iya bakin kokarin su ba dare ba rana don ganin sun faranta wa magoya bayan kungiyar rai nan da shekara mai zuwa inda kungiyar zata dawo gasar Firimiya lig a shekarar gaba.
Facebook Forum