Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biyan kudin fansa na iya arsasa sace mutane:Boube Namaiwa


Sojojin Najeriya (File Photo)
Sojojin Najeriya (File Photo)

Masu sharhi kan lamura suna tsokaci kan sace sacen al’umma da ya fara buwayar al’umma a Najeriya, da ya hada da sace limaman addinin Kirista uku da kuma wani babban jami’in soja a Kaduna.

A cikin hirarsu da Jummai Ali. Profesa Boube Na Maiwa na jami’ar Diop, Dakar, kasar Senegal ya bayyana cewa, ganin yadda wadansu suka rika yin haka a lokuta bayan ana bayansu kudin fansa, yana daya daga cikin dalilan da ake yawan garkuwa da jama’a. Yace neman kudin banza da arzikin daren daya na iya sa zauna gari banza shiga irin wadannan ayyukan.

Yace na biyu kuma, idan aka sami yanayi na tashe tashen hankali da ayyukan ta’addanci kamar yadda Najeriya ke fuskanta, to yana yiwuwa masu irin wadannan aika aikan su shiga sace wadanda suke gani suna iya hana ruwa gudu a al’amuran nasu. Yace irin wadannan mutanen suna kuma iya sace wadanda suke gani zasu iya samun kudi daga garesu domin sayen makaman da suke amfani da su ko kuma domin su yi garkuwa da su.

Rundunar sojin Najeriya ta sanar jiya Lahadi cewa, an sace Kanal Sama’ila Musa daya daga cikin manyan jami’an makarantar horas da sojojinta dake Jaji garin Kaduna, bayanda wadansu mutane da ba a san ko su wanene ba suka tare motar da yake ciki da iyalinsa, suka fitar da ita daga motar kafin suka shiga suka arce da shi.

Lamarin ya faru ne ranar asabar da misalin karfe bakwai da rabi na yamma. Hukumomi suna kira ga al’umma su sanar da ofishin jami’an tsaro mafi kusa idan suna da wani bayani dangane da lamarin.

Yan fashin dai sun arce ne a bakar mota kirar marsandi mai lamba. KUJ 154 TZ.

Ga cikakken bayanin Prof Boube Namaiwa

Fashin baki kan sace mutane a Najeriya:4:16
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG