A ranar 28 ga watan Yuni, lauyoyin Ganduje, wadand ke samun jagorancin E.O.B Offiong, suka nemi izinin su janye karar da suka shigar da Jaafar Jaafar da kamfaninsa kan dangane da wani bidiyo da ya wallafa, wanda suka yi zargin ya batawa gwamna Ganduje suna.
A watan Oktoban 2018, jaridar ta Daily Nigerian wacce mallakin Jaafar Jaafar ce, ta wallafa hoton bidiyon da ke nuna alamun gwamnan na jihar Kano yana karbar cin hancin daurin daloli daga wani dan kwangila yana durawa a aljihunsa, bidiyon da gwamnan ya musanta.
Hakan ya sa ya shigar da Jaafar Jaafar kara hade da kamfaninsa inda ya nemi a biya shi diyya kan bata suna da bidiyo ya yi masa, amma a baya-bayan nan lauyoyin Ganduje sun janye karar.
Karin bayani akan: Abdullahi Umar Ganduje, jihar Kano, Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, Nigeria, da Najeriya.
A nasa bangaren lauyan Daily Nigerian, Muhammad Dan Azumi, ya shigar da korafi, inda ya nemi kotun da ta ayyana zargin Ganduje a matsayin mara tushe tare da neman biyan diyyar miliyan 300 ga Jaafar Jaafar da kamfaninsa saboda bata masu suna da aka yi, kamar yadda jaridar ta Daily Nigerian ta ruwaito.
A cewar jaridar ta Daily Nigerian, Alkalin kotun S.B. Namalam, ya amince da janye karar da lauyoyin Ganduje suka yi, amma ya yanke hukuncin su biya Jaafar Jaafar da kamfaninsa naira dubu 800.