ABUJA, NIGERIA - A wani taron manema labarai da kungiyoyin suka kira a Abuja, jagoran tafiyar Suleiman Tambaya ya bayyana wa Muryar Amurka cewa, Arewa da sauran sassan kasar za su fito kwansu da kwarkwatansu su nuna rashin goyon bayan su ga duk ‘dan takaran da ba zai iya lissafin tushen arzikin sa ba, ko kuma yana da halin mantuwa da yawan kokwanto wanda alamu ne ta rashin natsuwa saboda haka bai kamata a zabe shi a zaben shekara 2023 ba.
Tambaya ya ce kungiyoyin za su tabbatar cewa an yi kamfe da mahawara masu tsafta da tarurruka na gari kafin lokacin zaben ya zo
Tambaya ya ce Kungiyoyin zasu ingiza samar da wata doka da za ta tilasta wa masu neman mukaman siyasa yin gwajin lafiyar su, sannan su bayyana sakamakon binciken a fili a matsayin sharadi na tsayawa takarar kowace kujera.
To sai dai masanin harkokin zamantakewa kuma mai fashin baki a al'amuran yau da kullum Abdurrahman Abu Hamisu, yana mai ra'ayin cewa wani abu ne da zai zama kamar da wuya a yanzu, duk da cewa akwai abin dubawa a cikin kiran domin abin takaici ne a ce matasan Arewa ba su san ciwon kansu ba, maimakon su nemi a bayyana masu matakan da za a dauka wajen kare hakkokin su, suna neman lafiyar shugabanni.
Hamisu ya ce, akwai lafiyayyu a karagar mulki da ba su tabuka komi ba, akwai kuma marasa lafiya da suka taka rawar gani.
Daya daga cikin matasan kasar Saleh Bakoro sabon fegi Damaturu ya ce an yi tuya ne an manta da albasa, saboda haka yana goyon bayan wannan mataki dari bisa dari. Saleh ya ce kasa tana cikin wani hali da ake bukatar lafiyayye ya rike shugabancinta.
Matasan sun ce lokaci yayi da za a tsamo masu halin mazan jiya irinsu Sir Ahmadu Bello, Nnamdi Azikiwe, Tafawa Balewa, Michael Opkara, Aminu Kano, Obafemi Awolowo, Umar Musa Ya'adua saboda a danka masu kasar a hannu.
Matasan sun ce sun gaji da rashin tsaro da yunwa da rashin alkibla da kasar ke tafiya akai.
Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda: