Najeriya ce ke bai wa Nijer Kashi 70 daga cikin 100 na wutar lantarkin da jama’ar kasar ke bukata sai dai gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta katse wutar a wani bangare na takunkumin kungiyar CEDEAO biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023, matakin da ‘yan fafutika suka ce ya saba wa doka dalili kenan suka kudiri aniyar garzayawa kotu kamar yadda jagoransu Alhaji Moustapha Kadi ya bayyana a taron manema labaran da suka kira.
Alhaji Moustapha yace ya zama wajibi jama’ar kasa da na duniya baki daya su sani duk da yake shugaba Bola Ahmed Tinubu na da ‘yancin katse wutar da kasarsa ke ba Nijer to amma matakin ya saba wa yarjejeniyar da ta shimfida wannan haraka sabili kenan gamayyar CODDAE ta lashi takobin kai koke a gaban kotu domin ta kwato wa ‘yan Nijer hakkinsu sai dai kawo yanzu ba su saka ranar shigar da karar ba.
Matakin na Tarayyar Najeriya ya haddasa tsayawar al’amura a fannoni da dama inda ‘yan Nijer ke tafka asarar dimbin kudade a kowace rana alhali tun kafin a girka ECOWAS kasashen biyu suka kulla yarjejeniyar kasuwancin wutar lantarki.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna