Hukumomi a Peru sun ce fursunoni 9 sun mutu a cikin makon nan a yayin rikicin da ya barke lokacin zanga-zangar neman inganta kiwon lafiya a sannadiyyar coronavirus.
Fursunonin gidan kason Miguel Castro sun yi zanga-zanga a ranar Litinin bayan da wasu 2 daga cikinsu suka mutu a sanadiyyar COVID-19 da ta bazu a gidajen kason kasar dan rashin kula. Akalla, fursunoni 13 sun mutu daga cikin 600 da suka kamu da cutar. Gwaje-gwajen da akayi ya nuna sama da ma’aikatan gidan kason 100 su ma sun kamu da COVID-19.
Baya ga bukatar inganta harkar lafiya, fursunonin sun bukaci shugaba Martin Vizcarra ya yi musu afuwa.
Tun a farkon makon nan ne shugaba Martin ya tsawaita wa’adin killace kai a fadin kasar har sai 10 ga watan Mayu, bayan da cutar ta dada yaduwwa a kasar, amma babu wani shirin da ya bayyana game da fursunin.
Facebook Forum