Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Yiwa Mata Fyade A Sudan Ta Kudu


 Tashin hankali a Sudan ta Kudu
Tashin hankali a Sudan ta Kudu

Hukumar dake lura da ganin an tabbatar da aiki da yarjejeniyar ya fitar da rahoto dake bayyana yadda sojojin ke yiwa kananan mata da mata fyade a Sudan ta kudu

Hukumar dake kula da yarjejeniyar shekarar 2015 ta Sudan ta Kudu, na neman duk bangarorin da yarjejeniyar ta shafa a kasar su yi aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sawa hannu watan da ya gabata.

A wata sanarwa da hukumar JMEC ta fitar jiya Litinin, da shugaban hukumar Festus Mogae ya nuna alamun yajejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnati da kungiyar ‘yan aware, da zummar samar da zaman lafiya a kasar da rikicin siyasa da na kabilanci yayi sanadiyar raba mutane miliyan hudu daga gidajensu tun watan Disambar 2013.

Mogae yayi kira ga dukkan bangarorin da rikicin ya shafa su yi aiki da alkwarin da suka ‘daukawa hukumar kasa da kasa dake kula da yarjejeniyar.

Gwamnati da kungiyar ‘yan awaren na nunawa juna yatsa kan saba dokokin yarjejeniyar da aka samar ranar 21 ga watan Disamba a birnin Addis Ababa na Habasha.

Hukumar dake lura da ganin an tabbatar da aiki da yarjejeniyar ya fitar da rahoto dake bayyana yadda sojojin ke yiwa kananan mata da mata fyade, da kuma zargin gwamnati na ci gaba da saka kananan yara cikin sojinta.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG