Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Tsige Magajin Garin Yamai Ya Sha Ruwa


Magajin Garin Yamai Hassan Seidu
Magajin Garin Yamai Hassan Seidu

Bisa ga wasikar da gwamnan jihar ya rubuta wadda shi Hassan Seidu ya karanta wa kansiloli tana cewar wa'adin makonni biyu da tsarin mulki ya basu na cigaba da shirin tsige magajin garin ya shude tun ranar 23 ga wannan watan, ke nan batun shigeshi ya wuce.

A cikin wasikar gwamnan fada cewa idan kansilolin sun cigaba da yunkurin to zasu sabawa doka lamarin da ka iya haifar masu abun da basu yi tsamnani ba.

Yanzu dai an dake taron kansilolin har zuwa wani lokacin da ba'a kayyade ba. Dama tun lokacin da kansilolin suka bada sanarwar shirin tsige magajin garin na kusa dashi suka fara kallon lamarin tamkar wata makarkashiyar siyasa.

Alhaji Nasamu Kada kusa a jam'iyyar Amin Amin wadda a karkashinta ne Hassan Sedu ya dare kujerar magajin garin Yamai nada irin wannan ra'ayin. Alhaji Kada yace mutane ne da suka yi kwangila da, suka shiga jam'iyyarsu amma suka koma jam'iyyun PNDS mai mulki da kawarta MNSD suna son su cimma burinsu.

Amma Alhaji Asumanu Muhammadou kakakin PNDS ya nisantar da jam'iyyarsa daga wannan alamarin.

Ita dai ma'aikatar magajin garin Yamai tayi fama da yaje-yajen aiki sakamakon rashin biyan albashin ma'aikata na watanni akalla biyar abun da kansiloli suka dauka wani kwakwaran hujjar tsige Hassan Seidu.

To saidai 'ya'yan jam'iyyarsa cewa suke rashin biyan ma'akata ba laifinsu ba ne. Sun ce laifin gwamnati ne ana dai son a shafa masu kashin kaza ne kawai.

Magajin Garin Yamai da magoya bayansa
Magajin Garin Yamai da magoya bayansa

Kakakin jam'iyyar PNDS Tarayya ya kara nanatawa babu hannunsu a ayyukan magajin gari saboda haka tsuntsun da ya jawo ruwa a kansa zai kare. Yace ba gwamnati ba ce take biyan albashin ma'aikatan kananan hukumomi, kuma abun mamaki ne a ce karamar hukumar birnin Yamai ta kasa biyan ma'aikatanta. Abun da ya faru shiririta ne kawai.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG