Yanzu haka dai ana arangama tsakanin matasan birnin Bamenda da jami’an tsaron Kamaru, wanda yayi sanadiyar mutuwar fararen hula guda hudu biyo bayan harbin kan mai uwa dawabi cikin taron jama’a da jami’an tsaron sukayi.
Gwamnan birnin Bamenda Adolphe Lele Lafrique, ya zagaya cikin birnin domin kwantarwa da al’uma hankali. Ya kuma nemi mutane da su bi doka da oda, ya kuma yi alkawarin gudanar da bincike domin gano wadanda ke hannu a rikicin domin hukuntasu.
Jagoran ‘yan adawar kasar Kamaru yayi kira ga shugaban kasa da rika sauraron kukan talakawan kasar. yanzu haka dai an rufe makarantu da masana’antu, biyo bayan kafa dokar ta baci da aka kafa.