Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fiye Da Kaso 40 Na ‘Yan Najeriya Na Samun Lantarkin Sa’o’i 20 A Kowace Rana-Ministan Lantarki


Ministan makamashi Adebayo Adelabu
Ministan makamashi Adebayo Adelabu

Ministan Lantarkin Najeriya, Cif Adebayo Adelabu, ya bayyana cewar fiye da kaso 40 cikin 100 na ‘yan najeriya na samun lantarki tsawon sa’o’i 20 a kowace rana.

Ya bayyana cewar an samu wannan nasara ne, sakamakon tsauraran matakan da gwamnati ta dauka na tabbatar da cewar ‘yan Najeriya sun mori tsayayyar wutar lantarki a koda yaushe.

Sanarwar da hadimin ministan akan harkokin yada labarai, Bolaji Tunji, ya fitar, a matsayin wani bangare na bikin ranar samun ‘yancin kai na bana tace an samu nasarorin ne da taimakon ajandar Shugaba Bola Tinubu ta sabunta fatan ‘yan Najeriya da nufin bunkasa tattalin arzikin kasar.

Adelabu ya kara da cewar an samu karuwar hasken lantarkin sakamakon tsauraran matakan da gwamnati ta dauka.

A cewarsa, shugaban kasar ya jima yana shelar cewa Najeriya na iya bunkasa tare da samun cigaba masana’antu, ta hanyar daidaituwar wutar lantarki.

Adelabu ya kuma jaddada bukatar ‘yan Najeriya su san cewar muhimmancin daidaituwar wutar lantarki abu ne da kasashen da suka ci gaba basa wasa da shi.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG