Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Macron Ya Rika Auna Kalamansa Kafin Ya Furta Su-Bolsonaro


Macron da Bolsonaro
Macron da Bolsonaro

Shugaban Brazil Jair Bolsonaro, ya ce kasarsa za ta karbi tallafin kudaden da kasashe mafiya karfi tattalin arziki na G7 suka ba ta domin ta yaki gobarar da ke ci a dajin Amazon mai dausayi, idan har Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya janye bakaken kalaman da ya yi.

A jiya Talata shugaban na Brazil ya fadawa manema labarai cewa, Shugaba Macron ya zarge shi da yin karya, yana mai cewa, sai ya janye kalaman, kafin nan sai a fara tattaunawa.

Shugaba Bolsonaro a cikin harshen Portuguese ya ce “da iznin Allah, za a samu maslaha wacce za ta gamsar da daukacin duniya, da shi kansa Shugaba Macron, wanda ya kamata ya rika tauna kalamansa kafin ya furta su, idan har yana son ya fice daga matsalar da yake ciki ta juya mai baya da al’umar kasarsa suka yi, kafin ya ce zai yi jayayya da mu.”

A dai taron da suka kammala a Faransa a farkon makon nan, shugabanin kasashen na G7 suka yi alkawarin ba da tallafin dala miliyan 20 domin a ceto dajin na Amazon, wanda ke da matukar muhimmanci ga duniya, saboda rawar da yake takawa wajen zuke gurbatacciyar iska.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG