Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FILATO: Wasu Masu Neman Takara Gwamna Na Barazanar Ficewa Daga Jam'iyar APC


Wasu masu neman takara karkashin jam'iyyar APC (Facebook/David Umahi).
Wasu masu neman takara karkashin jam'iyyar APC (Facebook/David Umahi).

Wasu mutane goma sha takwas dake neman takarar kujerar gwamnan jahar Filato a karkashin jami’iyyar APC, sun yi barazanar ficewa daga jami’iyyar tare da dimbin magoya bayansu, in har jami’iyyar bata dakile take-taken dora dan takara da basu amince da shi ba.

Kungiyar gamayyan masu neman tsayawa takarar gwamna a jahar Filato, karkashin shugabancin Chief Amos Gizo yace tun farko sun yanke shawarar amincewa su fidda dan takara su kuma hadu dukkansu su goya masa baya don tinkarar sauran jami’iyyu amma ba zasu lamunci gwamna ko shugabannan pati su dora musu wani ba.

Kungiyar ta kuma ja kunnen jami’iyyar da kar ta kuskura ta kirkiro wakilai wato delegates ba tare da amincewarsu ba.

A gefe guda kuwa, shugaban jami’iyyar APC a jahar Filato, Honarabul Rufus Bature yace zasu yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da adalci wa dukkan masu neman shiga takara.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG