Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Nigeria Ta Kara Wa'adin Yin Rajista Zuwa Karshen Wata


INEC
INEC

Biyo bayan koke koken da jama'a suka rika yi akan karancin lokacin yin rajistar zabe, hukumar zaben Nigeria ta amince da karin lokaci har zuwa karshen wannan watan tare da yiwa karin jam'iyyu 23 rijista.

Hukumar zaben Nigeria INEC ta kara wa’adin lokacin rajistar zabe daga ranar 17 ga watan nan zuwa 31 ga wata.

Hukumar ta dau wannan mataki don lura da yadda mutane ke fitowa don neman rajistar, yayin da wa’adin ya kusa karewa.

Ana wannan aikin na rijistar a kananan hukumomin kasar 774 da karin cibiyoyi 672.

Sanarwa daga kwamishinan wayar da kan masu kada kuri’a Muhammed Haruna, ta ce za a ci gaba da yin rajistar in ban da ranakun hutu kamar lokacin murnar babbar sallah.

Zuwa yanzu hukumar ta yiwa mutane miliyan 12,139,061, tun fara shirin a bara.

Mutane da dama da su ka fita domin samun rajistar sun bukaci karin wa’adin don hakan ya ba su damar samun katin saboda su zabi wanda su ke so a 2019.

Kazalika, hukumar zaben ta amince da yi wa karin jam’iyyun siyasa 23 rajista cikin adadin kungiyoyi masu neman rajistar 144.

Da wannan karin dai yanzu adadin jam’iyyun siyasa a Nigeria sun kai 91.

Daga wadannan jam’iyyu da za a dora kan takardar dangwala kuri’a, ba za a sake yi wa wata jam'iya rijista ba sai bayan zaben 2019.

A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG