Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Filato: An Yiwa Ofishin ‘Yan Sandan Garin Dangi Fashi


Wasu da ba a san ko su wanene ba sun fasa ofishin ‘yan sandan garin Dangi dake karamar hukumar Kanam a jihar Filato, inda suka kashe ‘dan sanda ‘daya da yin awon gaba da makamai.

Al’ummar garin Dangi sun bayyana fargabarsu ga abin da ka iya biyo baya, bayan da aka kashe ‘dan sanda tare da kwasar makamai daga ofishin ‘yan sandan garin.

Muryar Amurka tayi kokarin tuntubar jami’an ‘yan sandan jihar Filato don jin bayanai ya ci tura, inda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Terna Tyopev, ke cewa bai sami cikakken bayanai kan lamarin ba.

Sai dai kuma wasu mazauna garin da wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji ta zanta da su sun bayyana cewa, da missalin karfe biyu na dare mutanen suka kaiwa ofishin ‘yan sandan hari suka kwashe makamai tare da kashe wani jami’i guda ‘daya.

Yanzu haka dai komai na tafiya yadda ya kamata a garin Dangi, duk da yake akwai zaman fargabar abin da ka iya faruwa.

Domin karin bayani ga rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG