Masu fashin baki a fagen siyasa da demokaradiyya na ci gaba da sharhi kan darrusan da ‘yan Afrika ka iya koya daga wannan gangamin lumana da ya wakana ba tare da tarzoma ba.
Baya ga Amurkawa da suka shiga jerin gwanan zanga-zangar an kuma gudanar da makamanciyarta a kasashen Faransa da Birtaniya da Jamus da sauran kasashen Turai, domin nuna goyon baya ga batutuwan da suka haddasa gangamin lumanar. Masu gangamin dai sun bayyana ra’ayinsu ne dangane da wasu manufofi da ake sa ran gwamnatin sabon shugaban Amurka zai aiwatar wadanda ke da nasaba da kalamansa nay akin neman zabe.
Galibin kalaman dai sun shafi jinsin bil Adama da addinai da tattalin arziki da kuma sauran al’amura na hakkin ‘dan Adam.
Mallam Abbati Bako, masanin kimiyyar siyasa da lamuran dimokaradiyya, yace darasin da ‘yan Afirka zasu iya koya ga wannan gangamin lumana shine, a matsayin shugaban al’umma duk abin da za a fadawa jama’a ya zamanto gaskiya, kasancewar dimokaradiyya ta shimfida cewa kowanne ‘dan ‘kasa yana da tacewa a tsarin dimokaradiyya, idan har shugabannin Afirka zasu bi wannan tabbas za a sami zaman lafiya.
Duk da yake dai ba kasafai gangamin da kungiyoyin mata ke gudanarwa a Najeriya kan zo da yanayin tarzoma ba, amma malama Hauwa Ibrahim, tace matan Afirka musammanma na Najeriya, na da abin koya a zanga-zangar da ta wakana a Amurka. Inda tace tun daga yanzu matan ke gyarawa sabon shugaban kasar irin lafazin da yake da kuma nuna masa cewa ba zasu lamunta ba.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.