Masana harkokin tattalin arziki da cinikayya bisa tsarin addinin Islama daga kasashen da dama suka gabatar da kasidu kimanin tamanin.
Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II shi ya fara gabatar da makala yace cigaban da hadahar kudi bisa tsarin musulunci ya samu a Najeriya bai takaita kawai a bangaren bankuna ba su ma fannonin inshora da hannayen jari sun rungumi tsarin na musulunci.
Akwai gamsuwa ainun yadda hukumomi dake kula da hadahadar kudade suka karbi al'amarin bisa jagorancin babban bankin kasa da hukumomi irinsu SEC da NDIC sun bullo da kyawawan tsare-tsare da suka dace da addinin musulunci.
Mai masaukin baki Farfasa Binta Tijjani Jibril shugabar cibiyar nazarin hadahadar kudade da alamuran bankin musulunci ta Jami'ar Bayero tayi karin haske gameda makasudin taron.
Farfasa tace so ake a fayyacewa mutane shi tsarin hadahadar kudi da banki kan tasarin musulunci da anfaninsa wajen kawar da talauci da kuma dora kasa akan tattalin arziki mai karko wanda zai dace da addinin musulunci da al'adunsu. Tace ita harkar hadahar kudi a musulunci ta fi harkar banki. Tana da bangarori daban daban.
Inji Farfasa Jibril baicin taron, cibiyar ta dukufa da bada horo a fannoni daban daban na hadahadar kudade bisa tafarkin shari'ar musulunci.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.