Hukumar dake kula da wasan kwallon kafa ta nahiyar turai (Uefa) ta hukunta mai tsaron raga na kungiyar kwallon Kafa ta Juventus Gianluigi Buffon, a sakamakon laifin da ta sameshi dashi na munanan kalamai da basu dace ba kan alkalin wasa Oliver wanda ya hura wasan da kungiyar Juventus ta yi tsakaninta da Real Madrid, a gasar cin kofin zakarun turai (UCL) 2017/18 wasan Kusa dana dab da na karshe (Quarter Final) a watan Afirilu da ta gabata.
bayan da alkalin wasan ya bada bugun daga kai sai mai tsaron gida ga Kungiyar Real Madrid, a mintuna na karshe a wasan, wanda hakan ya janyo aka ba Buffon Jan kati bisa ga furucinsa ya fice daga wasan, an dai tashi a wasan juventus ta sha 3-1 a Bernabeu sai dai hakan bai bata nasara zuwa zagayen gaba ba sakamakon tun akarawar farko Real ta bita har gida ta Sha ta 3-0 inda jimillar kwallayen suka kama 4-3.
Uefa ta dakartar da Buffon ne daga buga wasanni har guda uku daga bangaren turai sakamakon wannan laifi.
Buffon ya buga wasansa na karshe a kungiyar Juventus a watan Mayu 2018 bayan ya shafe shekara goma sha bakwai a kungiyar.
Facebook Forum