Fatima Haruna Dan Waire - Wacce aka fi sani da ‘The Cruncy Box’ wadda ta ke abincin sayarwa da suka kunshi kayan tande-tande, da kayan abinci irin namu na gida dama na kasashen waje, inda ta zamanantar da sana’arta dai-dai da zamani.
Fatima ta ce babban abinda ya sa ta fara sana’a dai, a cewarta tun tana karama ta ke da sha’awar abinci, kuma a lokacin da ta fara tasowa sai ta lura cewa mafi yawan matan da ke kewaye da ita suna da sana’ar hannu, hakan ne yasa ta tashi tsaye wajan neman sana’a.
Kafin ta fara harkar abinci ta ce sai da ta fara sana’ar sayar da takalma da jakunkunan mata, amma hakar ta bata cimma ruwa ba, sai ta ga cewa sana’ar abinci ne ta fi bata sha’awa, kuma abinda ranta ke so kenan shine ta fara harkar abinci na kayan tande-tande amma a zamanance.
Ta ce ta fara sana’a da karamin jari inda mahaifiyarta ta ranta mata kudi, kuma ta fara ne da yin iya adadin da mabukaci ke bukata, malama Fatima ta ce a rana takan yi ‘meat pie’ ko ‘samosa’ akalla guda dari uku zuwa dari shida.
Daga cikin kalubalen da ta ke fuskanta ta ce akwai matsala, ta sai bayan mutum ya gama aiki sannan biyan kudin aikinsa ya zama jidali, don haka ne a yanzu bata aiki sai an biya ta kudinta sannan ta ke yi wa mutum abinci.
Amma daga karshe ta ce babban burinta shine ta bude gidan cin abinci na zamani, tare da jan hankalin matasa da su kama sana’a don su kauracewa yawan bani-bani, domin a wannan zamani an wuce wannan lokaci.
Facebook Forum