Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fatake Sun Yi Barazanar Sake Shiga Yajin Aikin Da Neman Kafa Kasuwannin Shiyoyi


Har yanzu tsuguni ba ta kare ba a kan batun sake shiga yajin aiki da hadakar kungiyoyin fatake ta Najeriya ta yi.

Fataken sun bayyana cewa, idan har gwamnati ba ta dauki kwararan matakai ba game da biyan bukatunsu da suka nema, ko shaka babu za su dau hukunci da babu gudu ba ja da baya lamarin da ka iya gurgunta ayyukan tattalin arziki a kasar.

Wannan lamarin ya samo asali ne daga yajin aikin gamagari da hadakar kungiyoyin fataken ta Najeriya ta fara a ranar 25 ga watan Febrairun wanda daga bisani ta janye bayan shiga tsakani da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi a madadin shugaban Najeriya bayan shafe kwanaki da yajin aikin.

Sai dai ya zuwa yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba duba da yadda gwamnatin Najeriya ta gaza cika alkawuran da ta dauka a cewar, shugaban hadakar kungiyoyin fatakan ta Najeriya, Dakta Muhammad Tahir.

Alhaji Sani Musa, da ke zaman shugaban kungiyar yan kasuwa da fatake reshen jihar Edo, ya ce da idan dan arewa 1 ya yi kuskure, shi a ke hukuntawa amma a yanzu sai a far wa duk dan arewa da aka sa a ido da zarar mutum daya ya yi laifi yana mai cewa, 'yan arewa na cikin hatsari matuka musamman ta fuskar tsaro a yankunan kudancin kasar.

Shi ma Alhaji Mustapha Ali, shugaban fataken kananan dabobbi kuma mai bincike a kungiyar fatake ta kasa ya ce kafa mu su kasuwar shiyya kan iyakar arewa da kudu ita ce mafita ga kashe-kashen mambobin su dake kai kaya can.

Duk kokarin ji ta bakin gwamna Yahaya Bello da ya shiga tsakani a baya da kuma gwamnatin Najeriya kan wannan lamari dai ya ci tura.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG