Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya kaddamar da rabon buhuna 21, 924 na shinkafa, a matsayin wani bangare shirin gwamnatin tarayya na wadata kasa da abinci.
Yayin da yake kaddamar da shirin a dandalin jama’a dake Katsina a jiya Lahadi, gwamnan ya bayyana cewar manufar shirin ita ce ragewa al’umma radadin kunchin rayuwar da suke fama da ita.
A cewarsa, shirin na nufin kaiwa ga bangarorin al’umma da dama musamman raunanan mata da kungiyoyin matasa da matakai daban-daban a mazabu da kananan hukumomi inda za’a karade jumlar rumfunan zabe 6, 652.
Ya kuma ankarar da cewar wannan shine karo na 2, da gwamnatin tarayya ke rabon kayan tallafi a jihar Katsina bayan da shugaban kasa ya samar da takin zamani ga manoman jihar domin yin amfani da shi a noman rani da damina.
Gwamna Radda ya kuma bayyana cewar a daminar bana a samu raguwar matsalar tsaro a jihar Katsina sabanin bara, domin an samu nasarar noma kaso 95 cikin 100 na gonakin jihar.
Dandalin Mu Tattauna